
Yadda Ake Chat Da Mace A WhatsApp Na Daya Daga Cikin Abubuwan Da Samari Da Yawa Suke Nema A Yau. Wasu Samari Suna Son Yin Chat Da Budurwa Amma Basa Sanin Wacce Hanya Zasu Bi Domin Jan Hankalinta Ko Sanya Ta Ji Dadin Hira Dasu.
Gaskiyar Magana Ita Ce, Yin Chat Da Mace Ba Wai Tura “Sannu” Ko “Yaya” Kawai Bane. Mata Da Yawa Suna Son Namiji Mai Iya Hira Da Daɗi, Nishadi, Da Kuma Respect.
Wasu Samari Suna Lalata Hira Tun Farko Saboda:
– Yawan Takura
– Yin Chat Mara Ma’ana
– Neman Soyayya Da Wuri
– Rashin Confidence
A Wannan Darasin, Zamu Nuna Maka Yadda Ake Chat Da Mace A WhatsApp Ta Hanyar Da Zata Ji Dadin Hira Da Kai Har Ta Rika Neman Jin Daga Gareka.
Idan Kana Son Sanin Yadda Zaka Sa Ta Rika Tunaninka Bayan Kunyi Chat, Karanta Yadda Zaka Sa Mace Ta Rika Tunaninka A Koda Yaushe.
Ka Guji Fara Chat Da Sannu
Daya Daga Cikin Manyan Kuskuren Da Samari Ke Yi Shine Fara Chat Da “Sannu” Ko “Hi” Kawai Ba Tare Da Wani Abu Mai Jan Hankali Ya Biyo Baya Ba.
Mata Da Yawa Suna Samun Irin Wannan Chat Kullum. Idan Kana Son Ta Lura Da Kai, Ka Fara Da Wani Abu Na Musamman Mai Ban Sha’awa.
Misali:
“Na Ga Status Dinki, Gaskiya Kin Burgeni Da Yadda Kike, Kinyi Kyau.”
Ko Kuma:
“Kina Daga Cikin Mutanen Da Bana Gajiya Da Chatting Dasu A WhatsApp.”
Irin Wannan Farkon Chat Na Sanya Taji Ita Ta Musamman Ce Sa’annan Tayi Maka Reply.
Masana Soyayya Sun Bayyana Cewa First Impression Na Da Muhimmanci Sosai A Conversation. Wannan Bayanin Na First Impression Ya Yi Karin Bayani Akan Tasirin Farkon Haɗuwa. Wanda Shine Yake Bayyana Irin Alaƙar Da Za’ayi.
Ka Kasance Mai Yawan Barkwanci
Mata Suna Son Namiji Mai Sanya Su Nishadi Da Barkwanci. Idan Hirarka Tana Sanya Ta Dariya, Zata Kara Jin Dadin Chat Da Kai.
Ba Lallai Sai Ka Nuna Soyayyarka Gare Ta Tun Farko Ba. Wani Lokaci Nishadi Da Nuna Kulawa Suke Ƙara Baka Damar Nasara A Wajenta.
Masana Sun Bayyana Cewa Positive Conversation Na Kara Attraction Tsakanin Mutane. Communication Psychology Ya Yi Karin Bayani Akan Muhimmancin Kyakkyawar Hira.
Kada Ka Yi Mata Interview
Wasu Samari Suna Yin Tambayoyi Da Yawa Kamar Masu Yin Interview: Misali,
“Ina Kike?”
“Me Kike Yi?”
“Wa Kike Tare Da Shi?”
“Yaya Akayi Haka?”
Irin Wannan Chat Na Sanya Mace Ta Gaji Gabadaya Da Kai.
Maimakon Haka, Ka Rika Hada Tambaya Da Nishadi Ko Ra’ayi Da Barkwanci.
Misali:
“Na Lura Kamar Kina Daga Cikin Mutanen Da Basu Ɓoye Fushinsu, Ko?”
Ko Kuma:
“Ki Fadi Gaskiya, Kina Daga Cikin Mutanen Da Suke Son Chat Da Dare Ko?”
Wannan Na Kara Sanya Hira Yayi Daɗi Ba Tare Da Takura Ba.
Ka Ringa Nuna Confidence A Lokacin Chat
Confidence Wato Ƙwarin Gwiwa Na Daya Daga Cikin Abubuwan Da Mata Suke Lura Dasu. Idan Kana:
– Yawan Rokonta
– Nuna Mata Tsoro
– Kokarin Faranta Mata Rai Fiye Da Kima
Wannan Duka Zai Rage Kimarka A Wajenta.
Ka Kasance Mai Natsuwa Da Self Respect A Lokacin Hira.
Masana Sun Bayyana Cewa Ƙwarin Gwiwa Na Kara Attraction A Relationship. Confidence Psychology Ya Yi Karin Bayani Akan Tasirin Confidence.
Idan Kana Son Karin Dabarun Jan Hankalin Mata, Karanta Sirrin Yadda Ake Sace Zuciyar Mace.
Ka Guji Yawan Yin Chat Da Mace

Wasu Samari Idan Sun Ganewa Yarinya Sai Su Dinga Damunta Da Chat Kullum Ba Kakkautawa Har Sai Sun Gaji Dasu.
Idan Kana Son Ta Rika Tunani Akanka:
– Kada Ka Rika Zama Available Kullum
– Ka Barta Ta Rika Missing Dinka
– Kada Ka Dinga Reply Nan Take Kullum
Wannan Na Kara Curiosity Da Interest.
Masana Sun Bayyana Cewa Mystery Da Space Na Kara Emotional Attraction. Interpersonal Attraction Ya Yi Bayani Akan Jan Hankali Tsakanin Mutane.
Ka Ringa Yi Mata Kalaman Yabo Wato Compliment
Mata Suna Son Compliment Amma Ba Kullum Ba, Kuma Ba Ga Jikinsu Ba.
Maimakon Kace:
– “Kin Yi Kyau” Kawai, Sai Ka Gwada: “Wato Salon Yadda Kike Tunani Yana Burge Ni.”
“Gaskiya Chat Dake Akwai Daɗi, Baki Yin Shirme.”
“Kina Daga Cikin Mutanen Da Hirarsu Ke Sanya Mutum Jin Dadi.”
Irin Wannan Yabo Da Ƙirari Na Taba Zuciya Fiye Da Cewa Kinyi Kyau Kawai.
Kada Ka Yi Gaggawar Neman Soyayya
Daya Daga Cikin Abubuwan Da Ke Korar Mata Shine Neman Soyayya Tun Farkon Chat, Ka Fara Gina: – Abota, Gina Nishadi, Yarda Da Aminci.
Da Zarar Ta Fara Jin Dadin Hira Da Kai, Soyayya Na Iya Samuwa A Hankali.
Masana Relationship Sun Bayyana Cewa Strong Friendship Na Taimakawa Wajen Gina Soyayya Mai Dorewa. Wannan Bayanin Na Friendship Ya Yi Karin Bayani Akan Kusanci Tsakanin Mutane.
Ka Rika Bata Lokaci Kana Sauraronta
Ba Chat Kawai Ke Jan Hankalin Mata Ba. Yadda Kake Fahimtar Abinda Take Fada Shima Yana Da Muhimmanci.
Idan Ta Fadi Abu: Ka Nuna Interest, Ka Ringa Tuna Abinda Ta Fada, Ka Bata Attention Dinka.
Mata Suna Son Namiji Mai Sauraron Su.
Idan Kana Son Fahimtar Alamomin Soyayya A Chat, Karanta Alamomin Da Zaka Gane Mace Tana Son Ka.
Kammalawa Daga Ƙarshe
Yadda Ake Chat Da Mace A WhatsApp Ba Wai Tura Sakonni Kawai Bane. Abu Mafi Muhimmanci Shine:
– Confidence
– Nishadi
– Respect
– Emotional Attention
– Kyakkyawar Hira
Idan Ka Koyi Wadannan Dabaru, Zaka Kara Jan Hankalin Mata Cikin Sauki Kuma Hira Dinku Zata Kara Dadi Har A Samu Kyakkyawar Soyayya.
Wace Hanya Ce Kuke Ganin Tafi Jan Hankalin Mata A WhatsApp? Ko Kuma Wane Kuskure Ne Samari Suke Yawan Yi A Chat? Ku Bar Mana Ra’ayoyinku A Sashin Comment Domin Mu Kara Tattaunawa.



