Kalaman Soyayya

Alamomin Mace Tana Son Ka: Yadda Zaka Gane Tana Sonka

Alamomin mace tana son ka abu ne da yake bukatar nazari mai zurfi domin mata sun kasance masu boye sirrin zuciyarsu faye da maza. Gano cewa mace tana kaunarka yana daya daga cikin manyan nasarorin da namiji zai iya samu a rayuwar soyayya, domin hakan yana ba shi damar sanin inda ya dosa. Sau da yawa, maza suna rasa damar samun mata na gari saboda rashin sanin wadannan alamun da suke bayyana a fili ko a boye. A cikin wannan cikakken jagoran, za mu fito da dukkan dabarun da mace take amfani da su wajen nuna shauki, ta yadda za ka iya gane hakan cikin kankanin lokaci ba tare da ka yi kuskure ba.

Gane Alamomin Mace Tana Son Ka Yake Da Muhimmanci

A Ilimin Psychology, Musamman Idan Muka Dubi Littafin The Definitive Book Of Body Language, An Bayyana Cewa Kashi 90 Na Sadarwar Dan Adam Tana Zuwa Ne Ta Hanyar Jiki (Non-Verbal Communication). Sanin Alamomin Mace Tana Son Ka Yana Taimakawa Namiji Wajen Kare Kimarsa Da Kuma Guje Wa Kaskanci. Idan Ka San Mace Tana Son Ka, Zai Kasance Da Sauki Wajen Tinkarar Ta Da Maganar Aure. Haka Kuma, Wannan Yana Taimakawa Wajen Gina Dangantaka Mai Karfi Wanda Babu Yaudara Ko Kuma Bata Lokaci A Cikinsa.

Yadda Zaka Gano Yanayin Soyayya Daga Bangaren Mace

Alamomin SoyayyaAlamar A ZuciyaLokacin Da Yafi Bayyana
Hada Ido (Eye Contact)Shauki Da Kuma KaunaLokacin Da Kuke Magana
Yawan Magana Ko KiraBukatar Kasancewa KusaLokacin Da Kuke Nesa Da Juna
Kishi (Jealousy)Tsoron Rasa Abin Da Ake SoLokacin Da Ta Ga Wata Mace
KyautaSadaukarwa Gare KaRanaku Na Musamman Koda Babu Dalili
Gabatar Da KaiNuna Alfahari Da KaiWajen Abokai Ko Yan Uwa

Alamomin Mace Tana Son Ka Ta Hanyar Kallon Ido Da Murmushi

Daya Daga Cikin Manyan Alamomin Mace Tana Son Ka Shi Ne Yanayin Da Take Kallon Ka. Ido Shi Ne Madubin Zuciya, Kuma Idan Mace Tana Kaunarka, Idanuwanta Ba Za Su Taba Iya Boye Hakan Ba.

Kallon Ido Mai Dauke Da Shauki

Lokacin Da Mace Take Son Ka, Za Ka Ga Tana Yawan Kallon Ka Kuma Idan Ka Kalli Idonta Za Ta Sauke Su Da Sauri Ko Kuma Ta Yi Murmushi. Wannan Alama Ce Ta Shauki Wanda A Turanci Ake Kira “Deep Gaze“. Ilimin Neuroscience Ya Bayyana Mana Cewa Idan Mutum Yana Kallon Wanda Yake So, Kwayar Idonsa Tana Kara Girma (Pupil Dilation). Idan Ka Lura Da Wannan A Wajen Mace, To Tabbas Tana Son Ka.

Murmushin Da Yake Kai Wa Ga Ido

Akwai Bambanci Tsakanin Murmushin Dole Da Kuma Murmushin Soyayya. Murmushin Da Mace Take Yiwa Wanda Take Kauna Yakan Kasance Mai Zurfi Wanda Har Yana Nuna Kananan Layuka A Gefen Idonta. Wannan Alama Ce Ta Tsantsar Farin Ciki Da Take Ji A Duk Lokacin Da Kake Kusa Da Ita.

Yawan Bukatar Ka Da Kuma Neman Lokacin Ka

Duk Macen Da Take SonKa Ba Za Ta Taba Bari Ace Rana Daya Ta Wuce Ba Tare Da Ta Ji Muryarka Ba. Wannan Shi Ne Babban Alama Daga Cikin Alamomin Mace Tana Son Ka A Wannan Zamanin.

  1. Tana Kasancewa Ta Farko Wajen Tura Maka Sakon Barka Da Safiya Ko Kuma Barka Da Dare, Ko Kuma Tayi Maka Flashing Har Sai Ka Kira.
  2. Na Biyu, Idan Ka Yi Posting A Social Media, Ita Ce Ta Farko Wajen Yin Like Ko Kuma Comment Domin Nuna Cewa Tana Bibiyar Rayuwarka.
  3. Tana Yawan Tambayarka Game Da Yadda Abubuwanka Suka Kasance Kuma Tana Sauraron Bayaninka Da Kyau.
  4. Idan Ka Yi Shiru Na Tsawon Lokaci, Zata Kira Ko Ta Turo Maka Da Sako Domin Tabbatar Da Cewa Kana Cikin Koshin Lafiya.

Sanya Ka A Cikin Tsarin Rayuwarta (Investment Model)

Alamomin Mace Tana Son Ka Yadda Zaka Gane Tana Sonka

A Ilimin Kasuwanci Da Kuma Psychology, Akwai Abin Da Ake Kira “The Investment Model“. Wannan Yana Nufin Mutum Yakan Fifita Kaunar Abin Da Abinda Yakeso. Idan Ka Ga Mace Tana Sanyaka A Tsarin Rayuwarta Tare Da Kai, To Wannan Yana Daga Cikin Manyan Alamomin Mace Tana Son Ka. Ga Yadda Zaka Gane:

  1. Tana Yawan Yin Amfani Da Kalmar “Mu” Maimakon “Ni” Idan Tana Maganar Abubuwan Da Za’ayi Nan Gaba.
  2. Zaka Ga Tana Tambayarka Game Da Burin Da Kake Son Cimmawa Kuma Tana Ba Ka Shawarwarin Da Zasu Taimaka Maka.
  3. Tana Kokarin Taimaka Maka Da Kudadenta Ko Kuma Basirarta Wajen Ganin Ka Ci Gaba A Rayuwa Ba Tare Da Ta Nuna Kyama Ko Gazawa Ba.

Zata Ringa Kishi Da Kai Sossai

Kodayake Kishi Idan Yayi Yawa Ba Shi Da Kyau, Amma Daga Ciki Alamomin Da Zasu Nuna Mace Tana Sonka Shine Kishi. Idan Mace Tana Son Ka, Bazata Taba Jin Dadin Ganinka Kusa Da Wata Mace Ba.

  • Canjin Yanayi: Za Ka Ga Yanayin Fuskarta Ya Canza Idan Kace Za Ka Je Wajen Wata Mace Ko Kuma Idan Tana Jin Kana Yabon Wata.
  • Tambayoyi Da Yawa: Za Ta Ringa Tambayarka Wanene Waccan Ko Kuma Me Ke Tsakaninku? Wannan Ba Rashin Yarda Bane, Tsoron Rasaka Ne Yake Sanya Ta Yin Hakan.
  • Neman Kulawa: Idan Ta Ga Hankalinka Ya Karkata Zuwa Wani Waje, Zaka Ga Yayi Kokarin Yin Wani Abu Da Zai Maido Da Hankalinka Gare Ita.

Zata Ringa Bada Labarinka Ga Yan Uwanta

Babu Macen Da Za Ta Kai Namiji Wajen Iyayenta Ko Kuma Aminanta Na Kusa Idan Ba Ta Da Soyayyar Gaskiya A Kansa. Wannan Shi Ne Mataki Na Karshe Na Alamomin Mace Tana Son Ka Wanda Ke Nuna Cewa Ta Amince Da Kai.

  1. Zata Ringa Bayyanawa Mahaifiyarta Ko Kanwarta Game Da Kasancewarka A Rayuwarta.
  2. Zata Ringa Gayyatarka Zuwa Taro Ko Kuma Bukukuwa Na Yan Uwa Domin Mutane Su San Cewa Kai Ne Wanda Take So.
  3. Zata Ringa Kokarin Karantar Da Kai Dabi’un Yan Uwanta.

Kula Da Abinci Da Kuma Lafiyarka

A Al’adarmu Ta Hausa Da Yankin Arewa Baki Daya, Mace Tana Nuna Soyayya Ne Ta Hanyar Dafawa Saurayi Abinci. Idan Ka Ga Mace Tana Tambayar Me Kake Son Ci Ko Kuma Tana Kawo Maka Abinci Mai Dadi, To Tabbas Zuciyarta Tana Gare Ka.

  1. Tana Kasancewa Cikin Damuwa Idan Taji Baka Da Lafiya Kuma Za Ta Yi Kokarin Ganin Ta Taimaka Maka Wajen Samun Sauki.
  2. Tana Kula Da Kananan Abubuwan Da Kake So, Kamar Kalar Da Kake So Ko Kuma Irin Shigar Da Take Burge Ka.

Karanta >>> Kalaman Soyayya Guda Da Ke Sace Zuciyar Mutum.

Kammalawa Kuma Shawarar Ƙarshe

Gano Alamomin Mace Tana Son Ka Yana Bukatar Ka Kasance Mai Lura Da Kananan Abubuwa. Soyayyar Mace Tana Da Dadi Idan Aka Sameta Ta Gaskiya, Kuma Wadannan Alamun Su Ne Hasken Da Zai Kai Ka Ga Samun Kyakkyawar Rayuwar Aure.

Idan Ka Lura Da Kashi 70% Na Wadannan Alamun A Wajen Mace, To Kada Ka Bata Lokaci, Ka Tabbatar Ka Nuna Mata Cewa Kai Ma Kana Kaunarta Domin Kar Ta Ji Kamar Ba Ka Damu Ba. Kuma Don Allah Karka Wulakantata, Karka Dauki Wannan Soyayyar For Granted Kayi Amfani Dashi Ka Cutar Da Ita.

Tambaya Ga Maza: Wace Alama Ce Kuka Fi Ganin Mace Tana Yi Idan Tana Son Namiji? Ku Kuma Mata, Shin Kun Taba Yin Daya Daga Cikin Wadannan Abubuwan Domin Nuna Soyayyarku Ga Namiji? Ku Bar Mana Ra’ayoyinku A Sashin Comment Domin Mu Tattauna Kuma Mu Taimakawa Juna.

Leave a Reply